March 27, 2023

​Najeriya: INEC Na Ci Gaba Da Bin Kadun Sakamakon Zaben Jihohin Da Suka Rage

 

Bayan sanar da sakamakon zaben akasarin jihohin da aka gudanar da zabe a Najeriya, a halin yanzu INEC tana ci gaba da bin kadun sauran sakamakon da ya rage.

Sakamakon da yafi daukar hankula dai a yanzu shi ne na jihar Adamawa, inda hukumar zaben ta ce zaben bai cika ba yadda ya kamata, a kan hakan an dage sanar da sakamakon sai bayan an sake bin kadun lamarin yadda zaben ya gudana.

A jihar Katsina kuwa dan takarar jam’iyyar PDP Sanata Yakubu Lado Dan Marke ya bayyana cewa ba su gamsu da yadda aka yi zaben ba, domin kuwa a cewarsa magudi aka yi a fili, kuma aka bi dukkanin hanyoyi domin murguda lamarin.

Ya ce an yi amfani da hanyoyi daban-daban na magudi domin tabbatar wa APC da nasara, kuma suna manyan hujjoji da dalilai kan hakan, kuma za su gabatar da su a gaban kotu domin sake bin kadun lamarin, a cewarsa.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Najeriya: INEC Na Ci Gaba Da Bin Kadun Sakamakon Zaben Jihohin Da Suka Rage”