November 23, 2023

​Najeriya: Farashin Man Fetur Ya Kara Hawa Zuwa Naira N630.63 A Cikin Watan Octoban Da Ya Gabata

 

Hukumar kididdiga ta kara a tarayyar Najeriya ta bada sanarwan cewa a cikin watan Octoban da ya gabata farashin man fetur ya karo a kasar zuwa naira 630.63 kan ko wace lita daga naira 195.29 a farkon wannan shekara.

Hukumar ta kara da cewa tana sanya ido a kan yadda farashin man yake jujjuyawa tun bayan zuwan sabuwar gwamnatin kasar a ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata.

Hukumar ta kara da cewa ya zuwa yanzu farashin man ya karu da kashi 222.92% tun ranar da shugaba Tinubu ya shelantar cire tallafi man fetur a ranar da ya karbi shugabancin kasar.

Labarin ya kara da cewa a cikin watan Satumban da ya gabata dai farashin ya tsaya kan naira N626.21 a matsayin farashinsa a gidajen man kasar. Ta kuma kara da cewa man yafi tsada a jihar Zamfara inda ake saida shi kan naira 657.27 kan ko wace lita.

 

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Najeriya: Farashin Man Fetur Ya Kara Hawa Zuwa Naira N630.63 A Cikin Watan Octoban Da Ya Gabata”