May 1, 2023

Najeriya: Fadar Shugaban Kasa Tace Buhari Ya Kawo Ci Gaba A Dukkan Bangarorin Rayuwa A Kasar.

Jaridar leader dership ta nakalto Adeisna yan cewa shugaban ya kawo ci gaba a dukkan bangarori na rayuwa ga mutanen kasar kama da tsaro, tattalin arziki, yaki da cin hanki da rashwa, manya-manyan ayyuka, jiragen kasa, hanyoyi, jiragin sama, tashoshin jiragen ruwa, wutan lantarki, gidaje, samar da ruwan sha, man fetur da gasa, gudanarwa, harkokin waje, wasannin, da tallafawa matasa, da kuma wasu da dama.

Kakakin fadar shugaban kasar ya kammala da cewa ma’aikatan watsa labarai a nan fadar shugaban kasa sun tattara bayanai dangane da irin ci gaban da shugaban ya kawo a cikin shekaru 8 mai zango biyu, sun kuma tabbatar da zancensa na cewa ba zai bar kasar nan kamar yadda ya same ta ba.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Najeriya: Fadar Shugaban Kasa Tace Buhari Ya Kawo Ci Gaba A Dukkan Bangarorin Rayuwa A Kasar.”