August 16, 2023

​Najeriya: Dattawan Arewa Sun Kirayi Tinubu Da Ya Gaggauta Janye Takunkumai A Kan Nijar

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta shawarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta janye duk wani takunkumin da aka kakabawa Jamhuriyar Nijar sannan a cigaba da tattaunawa.

In ba a manta ba, mun rahoto muku cewa, Nijeriya ta rufe dukkan iyakokinta da Jamhuriyar Nijar, sannan kuma ta katse wutar lantarki da dai sauran takunkumai.

A wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da hulda da Jama’a na kungiyar, Dakta Hakeem Baba Ahmed ya fitar a Abuja, ya shawarci Nijeriya da ta cire duk wani takunkumin da aka sanya wa Nijar, da nufin tilastawa gwamnatin Sojin kasar da su mika wuya ga bukatar ECOWAS. Yin hakan zai taimaka wajen samun fahimta cikin sauki.

Dakta Hakeem ya kara da cewa, ya kamata shugaba Tinubu ya tabbatar da “tsaron lafiyar shugaba Bazoum da iyalansa da kuma maido da tsarin mulkin Dimokuradiyya su zama muhimman abubuwa a gaban kungiyar ta ECOWAS.” Inji Baba Ahmed.

Kungiyar kuma ta yi watsi da bukatar amfani da karfin soji wajen dawo da mulkin Dimokuradiyya a Jamhuriyar Nijar inda ta ce, yin hakan ba zai haifar da kyakkyawan sakamako ba.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Najeriya: Dattawan Arewa Sun Kirayi Tinubu Da Ya Gaggauta Janye Takunkumai A Kan Nijar”