Najeriya: Bola Ahmad Tinubu Ya Rantsar Da Sabbin Ministocinsa.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya rantsar da sabbin Ministoci 45 da Majalisar Dattijai ta sahale masa ya nada.
An gudanar da rantsuwar ce a Fadar Shugaban ta Aso Rock da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, da safiyar Litinin.
Wadanda shugaban ya fara rantsarwa su ne Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi da na Iskar Gas, Ekperipe Ekpo da kuma Karamar Ministar Kwadago da Samar da Ayyukan yi Nkiruka Onyejeocha da ta Harkokin Mata Uju Kennedy, sai na Ilimi, Tahir Maman.
Kazalika, a rukuni na biyu kuma, Tinubu ya rantsar da Ministan Noma da Samar da abinci, Abubakar Kyari da na Harkokin Waje, Yusuf M. Tuggar da na Lafiya da Walwalar Jama’a, Ali Pate.
Sauran su ne Ministan Ruwa, Joseph Utsev da Karamin Ministan Mai, Sanata Heineken Lokpobiri.
Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya dora wa sabbin ministoci aiki da su cika burin ‘yan Nijeriya na samun wani sabon ci gaba ta fudkar tattalin arziki
Ya bayyana hakane bayan an rantsar dasu a bayaninsa
Ya ce gwamnatin ta zo a daidai lokacin da kasar ke bukatar gyara ta kowane fanni.
“Yan Nijeriya suna sa ran za ku taka muhimmiyar rawa kamar yadda muka alkawarta musu a lokacin yakin neman zabe. Daga rantsar da ku a yau, kun zama ministocin Tarayyar Nijeriya ba ministocin wata jiha ko yanki ba.