June 1, 2023

​Najeriya: Barayin Danyen Man Fetur Sun Yi Musayar Wuta Da Jami’an Tsaro A Jihar Delta

 

Al-ummar karamar hukumar Udu na jihar Delta sun shiga cikin tashin hankali a jiya a lokacinda jami’an tsaro a yankin suka yi ta fafatawa da barayen danyen man fetur a yankin.

Jaridar Leadership ta Najeriya ta bayyana cewa da farko jami’an tsaro sun kama wata mota dauke da danyen man fetur a cikin gari, daga baya wanda aka Kaman ya kaisu inda ya dauko man, a nan ne sai gungun barayin suka kore kungiyoyi masu sa ido wadanda gwamnatin ta azawa nauyin kula da wadanda suke satar mao a yankin, suka koresu daga yankin. A nan ne jami’an yansanda suka tattara ma’aikatansu zuwa wurin inda suka yi ta musayar wuta da marayin na lokaci mai tsawo kafin su kai ga rijiyoyin da suke satar man daga karshe.

Jami’an tsaro a yankin sun tabbatar da kama mutane biyu wadanda ake tuhama da aikin satar danyen man fetur a yankin kuma zasu gurfanar da su a gaban kotu idan sun kammala tattara bayanan da suka dace.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Najeriya: Barayin Danyen Man Fetur Sun Yi Musayar Wuta Da Jami’an Tsaro A Jihar Delta”