April 15, 2023
Najeriya: An Gudanar Da Taron Raya Ranar Kudus A Ofishin Jakadancin Iran A Abuja.

An gudanar da taron raya ranar kudus ta duniya a ofishin jakadancin JMI dake Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. Inda manyan baki daga bangarori daban daban suka sami halatan taron.
Masu jawani a taron sun hada da jami’an diblomasiyyar JMI a Najeriya da kuma wasu fitattun malamai da masana a kasar.
Taron ya bayyana muhimmancin tallafawa al-ummar falasdinu wajen yaki da yahudawan sahyoniyya wadanda suka mamaye kasarsu