November 22, 2023

Najeriya: Alkalai Ne Ke Sakin ‘Yan Boko Haram Bayan Kama Su

 

Manyan Shugabannin Ɓangarorin Tsaron Ƙasa, ciki har da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, sun bayyana a gaban Majalisar Tarayya, domin zama na musamman kan yadda za a daƙile matsalar tsaron da ke sake kunno kai, musamman ta Boko Haram da ke sake dannowa yanzu.

Waɗanda suka halarci gayyatar da majalisar ta yi masu, sun haɗa da Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Christopher Musa; Hafsan Hafsoshin Askarawan Najeriya, Taoreed Lagbaja da Hafsan Hafsoshin Sojojin Ruwa, Emmanuel Ogala.

Sauran sun haɗa da Hafsan Hafsoshin Sojojin Sama, Hassan Abubak da kuma Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun.

Da ya ke jawabi, Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya, Musa, ya ɗora laifin sake fantsamar ta’addancin Boko Haram kan alƙalan Najeriya.

Ya ce su ke da laifi, domin idan sojoji sun kama Boko Haram a hannu, sai alƙalai su sake su idan an je kotu.

Ya ce yanzu abin na nema ya kai har jami’an tsaro ba su ma so su kama ɗan Boko Haram.

©Hausa tv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Najeriya: Alkalai Ne Ke Sakin ‘Yan Boko Haram Bayan Kama Su”