October 5, 2021

NAFDAC TA GARGADI AL’UMMA KAN AMFANI DA KAJIN DA AKA SHIGO DASU DAGA KASASHEN WAJE

Daga Balarabe Idriss


Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa wato NAFDAC ta gargadi yan Nijeriya kan amfani da kajin da aka daskarar kana aka yi safarar su zuwa kasar.

Mai magana da yawun hukumar, Abubakar Jimoh ne yayi gargadin a yayin wata hira da yayi da kamfanin dillancin labarai ta Najeriya (NAN) a birnin Abuja.

Ya bayyana cewa irin wadannan kayayyaki ana ajiyar su ne ta hanyar amfani da wani sinadarin dake da illa ga lafiyar Dan adam.

Ya bayyana cewa wannan sinadarin shine sinadarin da ake amfani da shi wurin killace gawarwaki a mutuware.

Yayi kira ga yan kasar da su yi amfani da kaji na cikin Nijeriya maimakon amfani da wadanda aka shigo dasu daga kasashen waje.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “NAFDAC TA GARGADI AL’UMMA KAN AMFANI DA KAJIN DA AKA SHIGO DASU DAGA KASASHEN WAJE”