January 30, 2023

MU’UTAMAR A KATSINA, MIYE MAKOMAR HARKA ISLAMIYYA A NIGERIA?

Daga Amjad Mukhtar Imam


Bayan godiya ma Allah madaukaki, zanso mai karatu (mai hankali da zurfin tunani) ya bani yan wasu mintuna domin karanta wannan rubutu nawa.

 

A kwanakin da suka wuce ne mabiya Malam Zakzaki suka shirya taron mu’utamar a katsina, wanda aka gayyaci mutane daban daban a sassan jihohin Nigeria, kai harma da wajen Nigeria, wanda Alhamdulillah anyi taro lafiya an kammala lafiya.

 

Saidai wannan taro yabar baya da kura, wanda dayawan mutane a ciki da wajen harka suke ta bijiro da wata tambaya, wacce har zuwa yanzu basu sami amsar ta ba, tambayar itace: “Ina Malam Yakubu Yahaya Katsina” meyasa ba’a ganshi a wajen wannan taron ba?

A zahirin lamari wannan tambaya ce mai kyau da ake bukatar amsar ta.

 

Alhamdulillah na samu bincikawa tare da tambayar na kusa dashi Malam Yakubu Yahaya Katsina, akan shin menene sababin da ya hana Malam Yakubu Yahaya Katsina zuwa wannan taro, sai ya amsa mini da cewa ba’a gayyace shi bane, wannan itace amsar da babu ragi bare kari a cikin ta.

 

Bayan na samu wannan amsa ne sai muka tatttauna da wani dan uwa dalibin Ilimi a Hauza kan cewa: Shin menene ra’ayin ka akan wannan lamari? Sai yace: “Abu na farko shi kanshi tsara taron a Katsina anyi shine da manufa, manufar kuwa itace wulakanta shi Malam Yakubu Yahaya, shi yasa ma aka gama shiri da taro har aka tashi babu wanda ya gayyace shi, hasali ma sunyi taron ne ba tare da jin ra’ayin sa ko neman shawarar sa kan za’a kawo taron katsina ba.

 

Sai yaci gaba da cewa: “Babban mai laifi a cikin wannan lamari shine shugaban ita harka islamiyya din Sayyid, saboda ya dau akalar harka duka ya dankawa matar shi, wacce idan taso ka to ka rabauta, idan kuma tayi kiyayya da kai to babu wanda zayyi alaka da kai, Ita matar sayyid ta fitar da nata kiyayyan da take na Malam Yakubu a fili, kiyayyar da Sayid yake yi masa kuma sai masu zurfin tunani ne zasu gane, sbd dalilai na kamar haka:

 

1 – Da Syd yana son Malam Yakubu Yahaya da yasa an gayyace shi, koda kuwa matar sa bata son shi.

 

2 – Dole ne a yayin da ake gayyatan manyan baki aji daga bakin syd kafin ayi taron, mu kaddara sunzo masa da sunaye, idan da yana son Malam Yakubu Yahaya dole ne yace ya banga katin gayyatar waane ba.

 

3 – Mukaddara anyi taro an watse baisan da cewa ba’a gayyaci Malam yakubu ba, tofa a iya sanin da nayiwa syd sai ya nemi wadanda suka yi gayyata ya nuna musu kuskuren su.

 

Amma idan ka duba babu daya a cikin wadannan.

 

Ana yawan cewa: “Harka kayan syd ne da iyalan sa, to ni sai a ynxu na kara tabbatar da hakan hakane”

 

Wannan shine khulasar maganar dan uwa dan harka, hakan tasa na kasa yin shuru nayi wannan rubutu.

 

Daga karshe ina son muminai mukhlisai suyi duba cikin wannan lamari, sannan muji ra’ayoyin su akai, shin kuna ga irin wannan abu dake faruwa zai harfar ma harka da mai ido?

SHARE:
Labarin CIkin Hotuna, Makala 0 Replies to “MU’UTAMAR A KATSINA, MIYE MAKOMAR HARKA ISLAMIYYA A NIGERIA?”