February 15, 2023

Mutum hudu sun mutu a rikicin rashin Naira a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa rikici ya barke a sassan kasar, yayin da jama’a ke shan wahala wajen neman takardun kudi a bankuna, abin da ya haifar da asarar rayukan mutane akalla hudu a jihar Edo, kamar yadda jaridar Thenation ta ruwaito.

Haka zalika, an samu barkewar tarzoma a birnin Ibadan, yayin da al’umma da dama ke cigaba da bayyana fushin su, saboda karancin takardiun kudin.

Wannan dai na zuwa ne, yayin da kotun kolin kasar ta dage cigaba da ssauraron karar da wasu jihohi suka shigar gabanta, kan wa’adin ranar 10 ga watan fabrairu da CBN ta ayyana a matsayin ranar da zza a daina karbar tsoffin takardun kudi.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Mutum hudu sun mutu a rikicin rashin Naira a Najeriya”