Mutane sama da Miliyan 25 ne Ke Gudanar Da Tarukan Arbaeen A Karbala

Rahoton tashar Alfurat sun ruwaito cewa
Hukumomin birnin na Karbala sun sanar da cewa, tun daga makon farko na watan Safar ne dubban daruruwan mutane suka fara shigowa birnin, duk kuwa da cewa saboda yawan jama’a yasa ala tilas jama’a su rika ficewa daga birnin suna komawa yankunansu ko kasashensu, domin bayar da dama ga wasu su iya shiga domin yin ziyara.
Bayanan sun ce fiye da mutane miliyan 25 ne suka shiga birnin na Karbala domin gudanar da ziyara a hubbaren Imam Hussain (AS) a wannan karon.
A bangaren ayyukan tsaro kuwa, dubban jami’an tsaro ne a cikin kayan sarki suke gudanar da ayyukansu na tabbatar da tsaro a ciki da wajen birnin na Karbala, da kuma manyan hanyoyi daga larduna daban-daban na kasar Iraki da ke isa Karbala.