December 30, 2022

Mutane 4 sun mutu sakamakon fashewar wani abu a Kogi.

 

An samu fashewar wani abu da safiyar yau Alhamis a Okene, jihar Kogi, inda ake fargabar mutuwar a kalla mutane hudu, kamar yadda rahoton ƴan sanda ya bayyana.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, fashewar ta faru ne da misalin karfe 9 na safe.

Lamarin ya faru ne a kusa da katangar kofa ta biyu ta gidan sarautar Ohinoyi na Ibira, kan titin Kuroko, Okene.

Fashewar ta yi sanadiyyar ƙonewar wata mota da babura biyu.

Wani ganau ya ce bam ɗin ya tashi ne daga motar da abin ya shafa da kuma masu babura, inda nan take suka kashe masu tuka keken guda biyu.

An ga gawarwakin wadanda suka mutu a wurin da fashewar ta afku yayin da jami’an tsaro su ka rufe wurin.

“Ina cikin gida sai na ji karar fashewar wani abu, lokacin da na fito, sai na ga wata mota tana ci ds wuta tare da babura guda biyu kusa da kofa ta biyu ta fadar ta Ohinoyi.

“Fashewar ta yi yawa yayin da na ga gawarwaki uku kwance a kusa da fadar,” in ji wani ganau.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kogi, SP Williams Ovye-Aya, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana faruwar lamarin a matsayin “abin takaici ne matuka” kuma abin ban tsoro ne.

Ovye-Aya ya ce ‘yan sanda na kan gaba a lamarin domin tuni jami’an tsaro suka rufe yankin.

Ya ce an fara gudanar da bincike kan tashin bam din.

 

©Daily Nigeria.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Mutane 4 sun mutu sakamakon fashewar wani abu a Kogi.”