May 29, 2023

Mutane 2 Sun Mutu Sanadiyar Tashin Bam A Garin  Keffi Na Jihar Nasarawa

 

Mutane 2 Ne Aka Tabbatar Da Mutuwarsu Bayan An Ji Karar Tashin Bam A Garin Keffi Na Jihar Nasarawa A Safiyar Jiya Lahadi.

Jaridar Daily trusta ta nakalto wadanda suka ganewa idanunsu kuma basa son a bayyana sunayensu suna cewa bam din ya tashi ne a wani gida inda mutanen biyu suke haya. Kuma suna yawaita tafiya su dawo gidan.

 

Wasu kuma sun bayyana cewa mutanen biyu suna daga cikin wadanda hukumar DSS take nema kuma wata kila suna da labarin cewa jami’an hukumar sun yiwa gidansu kawanya ne sai suka tada bam suka kashe kansu.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Mutane 2 Sun Mutu Sanadiyar Tashin Bam A Garin  Keffi Na Jihar Nasarawa”