December 27, 2023

mutane 100 ne suka rasa rayukan su yayin wani hari da aka kai a jihar Filato

Farko dai ’yan ta’addan sun fara kai hari ga yankin Bokkos kafin daga bisani ya yadu zuwa wasu sassan yankin Barkin Ladi da Mangu.

A kalla dai ya zuwa yau Talata adadin mutanen da suke kwance a asibiti ya haura dari 3 bayan mumunan raunikan da suka samu yayin harin.

A lokacin da ya ziyarci yankunan da al’amarin ya faru da yammacin jiya Litinin, gwamnan jihar Filato Mr. Caleb Mutfwang ya yi alla wadai da wannan hari.

Ya ce ya kadu sosai da samun wannan labarin wanda ya yi sanadin mutuwar mutanen da ba su ji ba su gani ba a dai dai lokacin da ake tsaka da shagulgulan bikin Kirsimeti.

“Ina son na nanata cewa al’amarin ya isa haka, ba za mu taba amincewa da ci gaba da irin wannan halayya ta rashin hankali da rashin tunani ba na hare-haren babu gaira babu dalili, wannan abun takaici ne kuma abun kaico.”

Yayin ziyarar dai, gwamnan na jihar Filato yana tare ne da kwamandan rundunar Operation Save Heaven Major Janar Abdullsalam Abubakar. Kwamandan ya ce dakarun rudunarsa sun sami nasara fatattakar maharan, inda a lokacin suka sami nasarar samun wasu wayoyin hannun maharan.

“Ba za mu huta ba har sai mun kamo wadannan ’yan ta’adda, wanda yanzu haka wayoyin da muka samu sun fara ba mu haske a kan yadda za mu kamo masu laifin domin dai fuskantar hukunci.”

Yanzu haka dai an baza jami’an tsaro a yankunan guda uku, kuma tuni aka fara gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin tagwayen hare-haren

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “mutane 100 ne suka rasa rayukan su yayin wani hari da aka kai a jihar Filato”