October 16, 2021

Murnar haihuwar fiyayyen halitta: Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata matsayin ranar hutu

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ayyana ranar Talata 19 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu ga ma’aikata don murna da turawar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabin rahama Muhammad (S.A.W.A).

 

A wata takarda da ma’aikatar harkokin cikin gida ta Nijeriya ta fitar wacce ta samu sanyawar hannun maga takardan ma’aikatar, Dr. Shuaib Belgore ya sanar da ayyana ranar ta Talata matsayin ranar hutu na ma’aikata ya kuma bayyana cewa Ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya bada hutun a madadin gwamnatin tarayyar Nijeriya, kana kuma ya taya sauran al’ummar musulmi na cikin gida da waje murnar zagowar ranar haihuwar Annabin.

A lokaci guda kuma Ministan ya yi kira ga yan Nijeriya musamman mabiya Annabin da su kaurace wa aiyukan ta’addanci da taka doka da oda inda ya nemi da su yi koyi da kyawawan dabiu na Annabi muhammad (S.A.W.A).

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Murnar haihuwar fiyayyen halitta: Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata matsayin ranar hutu”