August 4, 2021

MUHAKKIK ALKARAKI

Daga Yakub Salisu

Shine Ali dan Hussain dan AbdulAliyul Amili Alkaraki, Wanda ya Shahara da MUHAKKIK ALKARAKI.  An haife shi a Shekara ta 868BH, a garin KarakNuh, Wanda yai shura (garin) mazaunin Yan Shi’a ne saboda samuwar wasu Mabiya Shi’a a cikin sojojin da suka Bude Sham.

Sannan garin na KarakNuh ya kasance maziyartar Malamai da Daliban Ilmi, Nan Shahidul Sani ya tafi neman Ilmi dashi da Mahaifin Sheikhul Baha’i.
Muhakakkik Alkaraki ya tafi Najaf Al’ashraf a shekara ta 909AH, ya bibiyi masu ilminta, har saida tauraronsa ya haska a bangaren Ilimi, har saida masu Mulkin Safawiyya ya fuskancesa, daga baya sai Shah (Sarkin Iran a Lokacin) ya nada shi a matsayin SHEIKHUL ISLAM a Isfahan Inda ya taka rawa a Tahirin Iran a Lokacin ……. Ya assasa makarantu na Tarihin Malamai da yadasu a garuruwan Iran. Sannan ya rubutawa Malaman Amil da Karak, Yana kiransu su taho zuwa Iran da haka suka yada Al’amuran Addini a Iran.
Lokacin da Shah ‘Dahamasib ya karbi mulki, sai ya sanar da Umarnin Mutane subi fatawowin muhakakkik Alkaraki, wanda ya karbi Al’amarin Wilayatul Faqih  Kuma Shah ya karba ya yadda da ita.
Bayan ya samar da Babban hidima a Iran, saiya koma Najaf Al’ashraf, Inda yayi Shahada ta dalilin guba kamar yadda Ma’abota Tarihi suka Tabbatar, a shekara ta 940BH.
Daga littafan daya rubuta akwai: Jami’ul Makasid (Yana daga Manyan littafan Fiqhun Shi’a), Risalatul Jafariyyah, Risalatul Isna Ashar fi Raddu alal Safawiyya.

Allah yayi masa rahama

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “MUHAKKIK ALKARAKI”