January 18, 2023

Mu’assasar Rasulul A’azam reshen jihar Borno ta gabatar da Mauludin Nana Fatima ƴar Manzo a birnin Maiduguri

Mu’assasar Rasulul A’azam reshen jihar Borno ta gabatar da Mauludin Nana Fatima ƴar Manzo a birnin Maiduguri.

A jiya Lahadi ne babbar qungiyar ƴan Shi’a zalla mai regista a Nahiyar reshen jihar Borno ta gabatar da Mauludin Sayyida Azzahra a Maiduguri, wanda shugaban ta na jihar Assheik Muhammad Albaqir ya yi jawabi a wajen taron, ya bayyana darojoji da matsayin Sayyida Azzahra, sannan ya taɓo ɓangaren rayuwar ta, inda ya bayyana cewa da al’umma zata yi koyi da rayuwar sayyida Azzahra da an magance matsaloli masu yawa na zamantakewar al’umma.

Daga ƙarshe aka karanta ziyara aka yi addu’a aka yi walima.

 

Daga Abubakar Aljafari Maiduguri.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Mu’assasar Rasulul A’azam reshen jihar Borno ta gabatar da Mauludin Nana Fatima ƴar Manzo a birnin Maiduguri”