Motar NSCDC dauke da kayan zabe zuwa Legas ta yi hatsari a Abuja

Wata motar jami’an tsaro da Civil Defence a Najeriya dake jigilar kayan zabe daga Abuja zuwa Legas ta yi hatsari a yammacin ranar Juma’a, jajibirin zaben.
Rahotanni sun ce hadarin ya afku ne a gadar Giri Roundabout da ke Abuja. Motar na dauke da jami’an NSCDC zuwa Legas.
A cikin wani faifan bidiyo a shafukan sada zumunta, an ga mutane suna taimakawa wajen Kwashe takardu da ake zaton kayan zabe ne da suka zube a kasa.
Wani mutum da ya yi magana a faifan bidiyon ya ce wasu daga cikinsu sun samu raunuka inda ya kara da cewa daya daga cikinsu ya samu rauni a kai.
Sai dai ya kara da cewa an dauke wasu manyan jami’an NSCDC zuwa wani waje daban.