September 2, 2021

Ministocin Da Aka Sauke: Da yiwuwar wasu su bi bayan su

Daga Musa Sanda Nguru
Biyo bayan sauke wasu ministoci guda biyo da Shugaba Buhari yayi a yan kwanakin nan ana kuma sake hasashen yiwuwar karin wasu su bi bayan su duba da kalamin shugan yayin sauke ministocin biyu.
Tuni dai mai magana da yawun shugaban kasa yayi bayani ga manema labarai cewa Shugaba Buhari ne kadai ya san dalilin sauke Ministocin biyu; Mohammed Sabo Nanono da Injiniya Saleh Mamman amma dai masana sun alakanta hakan da rashin kwazon ministocin wanda kuma alamu na nuna yiwuwar wasu karin ministocin zasu bi bayan su.
Shugaban kasar dai ya shelanta sauke ministocin biyu ne a ranar Laraba, wannan dai shine karo na farko da shugaban ya dau matakin sauke ministoci kafin cikar wa’adin su tun zaman sa shugaba a shekarar 2015.
Ministocin dai guda biyu tuni aka maye gurbin su daTsohon Ministan muhalli Dakta Mohammed Mahmud Abubakar inda ya maye gurbin Mohammed sabo Nanono, da kuma Tsohon karamin Ministan aiyuka Injiniya Abubakar D Aliyu inda ya maye gurbin injiniya Saleh Mamman.
Jaridar “Daily Trust” ta wallafa a shafinta cewa ta samu rahoto kan saukar da ministocin inda kuma tace ta jiyo daga majiya ta sirri cewa fadar shugaban kasar ta dau aniyar sauke karin wasu ministoci nan gaba kadan.
Kana kuma rahotanni sun bayyana cewa yayin daukar matakin saukar da minstocin biyu Shugaba Buhari yace matakin zai cigaba wanda hakan ke nuna yiwuwar karin ministoci zasu biyo sahun wadanda aka dakatar.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Ministocin Da Aka Sauke: Da yiwuwar wasu su bi bayan su”