September 1, 2023

Ministan Sufuri ya dakatar da aikin “Nigeria Air”

 

Ministan sufuri Malam Festus Keyamo a jiya Alhamis ya bayyana dakatar da aikin kamfanin jirgin sama na Nigeria Air mallakin kasa.

 

Ministan ya bada wannan umarnin ne a yayin ziyarar aiki zuwa filin tashi da saukan jirgin kasa-da-kasa na jihar Legas inda ya samu rakiyar Manaja na hukumar FAAN, Malam Kabiru Yusuf Mohammed.

Minista Keyamo ya kara da dakatar da wasu warjejeniyar da tsohon ministan da ya gabace shi ya rattaba hanu. Inda yace komai zai cigaba da zarar ya tattauna da Shugaba Bola Tinubu.

A bayaninsa, Minista Keyamo ya ce akwai abubuwan la’akari kan jirgin Nigeria Air da aka fitar kwanakin baya don kama aiki. Inda yace wasu binciken sun nuna cewa tsohon jirgi ne na tsahon shekaru, kana kuma ya yi aiki a kasar Habasha.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Ministan Sufuri ya dakatar da aikin “Nigeria Air””