June 6, 2024

Ministan Kudi Ya Gana Da Shugaba Tinubu akan Mafi Karancin Albashi,

 

Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, zai iya gabatar da samfurin sabon mafi karancin albashi

Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, zai iya gabatar da samfurin sabon mafi karancin albashin ma’aikata ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan ganawa da shugaban kasar, Ministan ya ce babu wani abin fargaba.

A ranar Talata, 4 ga watan Yuni ne shugaban ya umurci ministan da ya gabatar masa da kudaden da ake kashewa na sabon mafi karancin albashi a cikin sa’o’i 48.

Ana sa ran samfurin zai samar da ci gaban tattaunawa tare da ƙungiyar ƙwadago.

Ministan Kudi ya zo Villa ne tare da Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu.

Ko da yake bai yi karin haske kan ajandar ganawar da shugaban kasar ba, mai yiwuwa ba za a rasa nasaba da tsarin da shugaban kasar ya nema a ranar Talata ba.

Taron kwamitocin uku ya kasa tattauna muhimman batutuwa a ranar Laraba sakamakon gazawar tawagar gwamnatin tarayya wajen gabatar da wani sabon adadi ga kungiyar kwadago.

Fassarar: Mohammad Baqir.

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Ministan Kudi Ya Gana Da Shugaba Tinubu akan Mafi Karancin Albashi,”