May 16, 2023

Ministan Harkokin Wajen Syria Ya Isa Saudiyya Domin Halartar Taron Share Fage Na Kungiyar Kasashen Larabawa

 

Jirgin da yake dauke da ministan harkokin wajen kasar ta Syria Faysal Mikdad ya sauka a filin saukar jiragen sama na Sarki Abdulaziz dake birnin Jiddah, domin halartar taron share fage na kungiyar kasashen larabawa da za a yin an da kwanaki uku masu zuwa.

Daga cikin masu rufawa Mikdad baya da akwai mataimakinsa Dr. Ayman Susan da shugaban ofishinsa Jamal Najib, sai kuma jami’in watsa labaru Dr. Butrus al-Hallaq.

Da yake Magana da ‘yan jarida a filin saukar jiragen saman, Faysal Mikdad ya ce; Jigon da aka bai wa wannan taron shi ne; Aiki tare a tsakanin larabawa,don haka muna tsinkayo yadda za mu yi aiki tare.”

Faysal Mikdad ya kuma ce: Mun zo nan ne domin mu yi aiki da ‘yan’uwanmu larabawa saboda mu fuskanci kalubalen da yake a gabanmu.

Faysal Mikdad ya kara da cewa; Wannan dama ce da za mu fadawa ‘yan’uwanmu larabawa cewa, gaba muke hangowa ba abinda ya faru a baya ba, kuma da akwai kalubale mai yawa a gabanmu da za mu tattauna shi.

Mikdad ta sami kyakkyawar tarba daga jami’an ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Saudiyya

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Ministan Harkokin Wajen Syria Ya Isa Saudiyya Domin Halartar Taron Share Fage Na Kungiyar Kasashen Larabawa”