May 28, 2024

Ministan harkokin wajen Spain yayikira ga sauran kasashe 26 na Tarayyar Turai da su goyi bayan kotun kasa da kasa

Jaridar ahlulbaiti ta ruwaito daga tashar Al-Mayaden ta turanci cewar,

Ministan harkokin wajen Spain Jose Manuel Albares ya bayyana cewa yana da niyyar yin kira ga sauran kasashe 26 na Tarayyar Turai da su goyi bayan kotun kasa da kasa a hukumance da kuma daukar matakin tabbatar da “Isra’ila” ta mutunta hukuncinta.

“Zan nemi sauran abokan huldar 26 da su bayyana goyon bayansu ga Kotun Duniya da kuma hukuncin da ta yanke, idan Isra’ila ta ci gaba da yin sabanin ra’ayin Kotun, za mu yi kokarin daukar matakan da suka dace don aiwatar da hukuncin.” ya sanar da manema labarai a Brussels yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwarorinsa na Ireland da Norway.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Ministan harkokin wajen Spain yayikira ga sauran kasashe 26 na Tarayyar Turai da su goyi bayan kotun kasa da kasa”