August 19, 2023

​Ministan Harkokin Waje Iran Ya Isa Birnin Riyadh A Wata Ziyarar Aiki A Saudiyya

 

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya isa birnin Riyadh a ziyararsa ta farko a Saudiyya tun bayan da kasashen yankin biyu suka amince da maido da huldar diflomasiyya a cikin watan Maris.

Amir-Abdollahian wanda ke jagorantar wata babbar tawaga a yau Alhamis ya tashi daga Tehran zuwa babban birnin kasar Saudiyya domin yin wata ziyarar aiki ta yini guda bisa gayyatar da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya yi masa.

Ana sa ran babban jami’in diflomasiyyar na Iran zai tattauna da Farhan da wasu hukumomin Saudiyya kan alakar da ke tsakaninsu da kuma batutuwan da suka shafi kasashen musulmi da kuma ci gaban yankin da kasa da kasa.

Jakadan Iran a Riyadh Alireza Enayati shi ma yana tare da Amir-Abdollahian kuma zai fara aikinsa a hukumance.

A cikin watan Yuni, Iran ta sake bude ofishin jakadancinta a Riyadh a hukumance

 

©VOH

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Ministan Harkokin Waje Iran Ya Isa Birnin Riyadh A Wata Ziyarar Aiki A Saudiyya”