January 9, 2023

Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ya Bada Umarnin Cire Tutocin Falasdinu

Ministan tsaron gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila ya umarci ‘yan sanda da su cire tutocin Falasdinu daga wuraren taruwar jama’a

Sabon ministan tsaron gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila Itamar Ben Gafir a jiya Lahadi ya umarci ‘yan sandan Haramtacciyar kasar Isra’ila da su cire tutocin Falasdinu a duk wuraren taruwar jama’a, kuma wannan shi ne mummunan mataki na baya-bayan nan da sabon ministan ya dauka, inda a mako guda da ya gabata ya dauki matakin keta hurumin Masallacin Aqsa.

Ben Gvir ya bayyana cewa: Daga tutar Falasdinu yana matsayin wani mataki ne na goyon bayan ta’addanci, duk da cewa dokar Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta fito fili ta haramta tutocin Falasdinu ba

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ya Bada Umarnin Cire Tutocin Falasdinu”