August 21, 2023

Me Ya Sa Kasashe Da Dama Suke Sha’awar Shiga Tsarin BRICS

Shugabannin kasashen BRICS wato Brazil, Rasha, Indiya, China da South Africa za su yi ganawa karo na 15 a kasar Afirka ta Kudu nan ba da dadewa ba, lamarin da ya jawo hankalin kasashen duniya, musamman ma kara shigar da kasashe cikin tsarin BRICS.

An ruwaito bangaren Afirka ta Kudu na cewa, yanzu kasashe fiye da 40 suna fatan shiga tsarin na BRICS, wasu fiye da 20 daga cikinsu kuma sun gabatar da bukatarsu a hukumance. Anil Sooklal, wakilin musamman na Afirka ta Kudu mai kula da harkokin BRICS ya bayyana yayin da yake zantawa da wakilin CMG cewa, kasashe da dama sun bayyana fatansu na shiga tsarin na BRICS, lamarin da ya nuna cewa, kasashen duniya suna da imani kan yadda BRICS suke ba da jagora wajen daidaita batutuwan kasa da kasa. To, me ya sa haka?

Idan muka yi bitar tarihin hadin gwiwar BRICS, za mu fahimci cewa, neman samun bunkasuwa shi ne mafi muhimmanci. Alkaluman da kamfanin Acorn Macro Consulting na kasar Ingila ya gabatar a watan Maris na bana sun shaida cewa, a shekarar 2022 da ta wuce, adadin jimillar tattalin arzikin kasashen BRICS ya wuce na kungiyar G7 cikin tattalin arzikin duniya.

Tsarin hadin gwiwar BRICS ya taka muhimmiyar rawa wajen ba da jagora kan yin hadin kan kasashe masu tasowa da kuma kara azama kan tafiyar da harkokin kasa da kasa. Kasashen na BRICS suna mutunta ikon mulkin kan juna, da muradun tsaro da raya kasa, suna kuma nuna adawa da siyasar fin karfi, da tunanin yakin cacar baki da yin fito-na-fito tsakanin kungiyoyi. Haka kuma, sun kafa cibiyar nazarin allurar rigakafin cututtuka ta BRICS, a kokarin yaki da cutar COVID-19 tare.

Kafofin yada labaru na kasashen duniya na ganin cewa, kasashen BRICS sun gabatar da sabon tunani da wayar da kan kasashen duniya dangane da sabuwar odar kasa da kasa, wadda ta sha bamban da odar kasashen duniya da ke karkashin laimar kasashen yammacin duniya.

 

©cri

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Me Ya Sa Kasashe Da Dama Suke Sha’awar Shiga Tsarin BRICS”