October 11, 2023

Me ya sa hukumar leken asirin Isra’ila ‘Mossad’ ta gaza hango shirin harin Hamas?

Duk da matsayin Mossad na zama daya daga cikin manyan hukumomin leken asiri a duniya, amma ba ta iya gano mummunan harin da abokan gaban Isra’ila suka shirya kai mata ba.

 

Daga Paul Salvatori

 

Yanayin shammata na kai hari cibiyoyin soji na Israi’a da wasu garuruwa da ke kan iyakar ƙasar da Gaza da mayaƙan Hamas suka yi, ya sanya ayar tambaya kan yadda babbar hukumar leƙen asirin Isra’ila ta gaza gane shirin da kuma tantance abin da ya faru a karshen mako.

 

Tambayar da ta fi ɗaukar hankali ita ce, ta yaya Mossad, babbar hukumar leken asirin Isra’ila, wacce ke da fasahohi da na’urar leƙen asiri iri daban-daban, kana wacce ta daɗe tana dogaro kan kutsen da take yi cikin ƙungiyoyin Falasdinawa mayaƙan sa-kai don tattara bayanai kan ayyukan kungiyoyin, ta gaza gano shirin kai mata harin.

 

Irin manyan hare-haren da mayaƙan Falasɗinawan suka ƙaddamar ta ƙasa da sama da kuma cikin teku a lokaci guda bai kamata ya wuce ba tare da an ankara ba.

 

Ta yaya Mossad ya gaza samun labarin hare-haren?

 

“Fasahohin leƙen asiri da kuma na’urorin sa ido na Isra’ila sun matuƙar yin ƙasa a gwiwa wajen gano hare-haren (balle su iya dakatarwa), kamar yadda Antony Loewenstein, marubucin littafin ‘Palestine Laboratory’- wani littafi da ya yi cikakken bayani kan ci-gaban fasahar leƙen asiri na Isra’ila ya shaida wa TRT World.

 

“Sannu a hankali, za a iya samun sakamako hakan a cikin tsarin siyasa da kuma ayyukan sojin Isra’ila, amma babu tabbas ko hakan zai yi tasiri sosai kan masana’antar kera makamai na Isra’ila, wanda tuni matsayinsa ya yi girma a ‘yan shekarun nan.”

 

Loewenstein ya ƙara da cewa: Duk Ƙasashen Yammacin Duniya suna goyon bayan Isra’ila kuma za su so su goyi bayan Yahudawa ta hanyar sayen makaman ƙasar tare da mara mata baya kan kisan gillar da ta yi a Gaza.

 

Sai dai a ƙoƙarin martaba sunanta da wuya Isra’ila ta fito fili ta bayyana gazawarta a fannin leƙen asirin da ta yi, duk kuwa da ire-iren na’urorin zamani na leƙen asirin da take da su.

 

Masu nazari kan lamarin na ci gaba da sharhi kan abubuwan da ka iya zuwa su dawo.

 

Wata mahangar ta yi nuni da cewa Isra’ila ba ta ankara da wuri ba saboda tunanin cewa Hamas ta yi rauni, sakamakon mamayar da Isra’ilan ta yi wa Gaza a tsawon shekaru, don haka Isra’ila ba ta yi zaton za a iya kai irin wannan ƙazamin harin ba, a ganinta ta fi fuskantar barazana daga ƙungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran da ke Lebanon.

 

Ana iya cewa Hamas ta yi amfani da fahimtar da aka yi mata, inda sannu a hankali ta fara aiwatar da shirinta na kai hari – tun daga ƙera makaman roka da ta harba a garuruwan Isra’ila da rushe gine-gine da wata babbar katangar waya da ta raba Gaza da Isra’ila- ba tare da samun martanin nan take daga birnin Tel Aviv ba.

 

Wani nazari na daban ya yi nuni cewa Isra’ila ta gaza gane tare da raina wayon irin ƙarfi da iya samar da makaman da Hamas ke da shi.

 

“Isra’ilawa suna sane da irin mummunar ƙiyayya da Hamas ke yi musu,” a cewar wani rahoto da Washington Post ta wallafa.

 

“Sai dai sun raina wayo da basirar abokan gabar tasu. Wannan abu ya nuna irin mummunar ɓarnar da za su iya yi da ba a taɓa zato ba,” in ji rahoton.

 

A zaton Isra’ila girman kan da take yi wa Falasdinu yana da nasaba da hakan.

 

Maimakon su dauki darussa na jajircewa da fafutukar da Falasdinu ta nuna wa duniya a tsawon shekarun da suka shude, da ke nuna dabaru na aiwatar da abubuwa cikin bazata sai suka fi mayar da hankali kan ƙrfin soja, don kawar da hankali daga kan waccar barazana.

 

Ko rikicin cikin gida da Isra’ila ke fama da shi, ya taka rawa wajen hana ta daukar matakin da ya dace don dakile harin?

 

Nazari na uku na marubuncin ya yi imanin cewa akwai yiwuwar an bar harin ya faru, la’akari da cewa Mossad ta fahimci yanayin da duniya ke ciki wanda ya ci karo da gwamnatin addinin Yawudanci na gwamnatin Netanyahu.

 

Hakan na nufin cewa akwai yiwuwar Mossad ta na sane ko kuma tana da bayanai game da harin na Falasdinawa, amma saboda rashin hadin kai da fahimta ta gaza bayyana irin wannan bayanai wa Netanyahu.

 

Ko ma menene dalilan Isra’ila ko ita kanta Mossad wacce ta kasa gano harin balle ta iya dakatar da shi,

 

Amma abu ne mai kamar wuya a ce Isra’ila “ta bari hakan ya faru”, in ji David Miller, Babban Jami’in Bincike a Cibiyar Musulunci da Harkokin Duniya ta Istanbul.

 

A cewar Miller, “babban abin kunya ne a ce kungiyoyin adawa na (Falasdinawa), wadanda ba a iya kwatanta su da kungiyoyin ‘Hamas’ a fili ba, su samu dama a fili – da kuma yadda suke so – su fasa gidan yarin Gaza tare tarwatsa sansanonin Isra’ila 10 da kuma yankunan matsugunansu 20”.

 

“Irin mummunan raunin da dakarun Isra’ila suka ji,” a cewar Miller, ya yi yawa ciki, har da kwamandoji da manyan hafsoshi, sannan an kama wasu wuraren.

 

Kwanaki uku kenan da faruwar lamarin kuma kafofin yada labaran Isra’ila na ci gaba da ba da rahoton cewa ana ci gaba da gwabza fada a garuruwan Isra’ila”.

 

Babu dai tabbacin kan yaushe za a kawo karshen rikicin, sai dai wani abu daya da aka tabbatar shi ne: a cikin ‘yan kwanakin nan Falasdinawa sun yi nuni kan cewa a tsaye suke da manyan makamai wajen durƙusar da ƙarfin soji.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Me ya sa hukumar leken asirin Isra’ila ‘Mossad’ ta gaza hango shirin harin Hamas?”