June 20, 2023

MDD Zata Jagoranci Tattaunawa Don Gudanar Da Zabubbuka Cikin Watanni Masu Zuwa A Libya

Wakilin MDD na musamman a kasar Libya ya bayyana cewa zai gaggauta tattaunawa tsakanin yan siyasa a kasar Libya don tabbatar da cewa an gudanar da zabubbuka a cikin yan watanni masu zuwa.

Jaridar ‘ArabNews’ ta kasar Saudiya ta nakalto Abdullahi Bathily yana fadar haka a gaban kwamitin tsaro na MDD a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa kara dage lokacin zabubbuka a kasar Libya zai zama babbar masibfa ga kasar da kuma kasashe makobta.

Ya kuma kara da cewa babban nasarar da aka samu na fahintar juna tsakanin majalisun dokoki biyu na kasar yana da matukar muhimmaci, amma kuma bai wadatar wajen tabbatar da an gudanar da zaben kamar yadda aka tsara cikin amince ba.

Bathily ya ce za’a sake gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu ko da kuwa wani dan takara ya sami kashi fiye da 50% a zagaye na farko, har’ila yau ba za’a gudanar da zaben majalisar dokokiba sai an kammala da na shugaban kasa.

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “MDD Zata Jagoranci Tattaunawa Don Gudanar Da Zabubbuka Cikin Watanni Masu Zuwa A Libya”