September 16, 2023

MDD Ta Mayar Wa Da Amurka Martani Akan Yankin Tudun Golan Dake Karkashin Mamayar HKI

 

Bayan da jakadiyar Amurka a MDD ta bayyana cewa; gwamnatin Joe Biden tana aiki ne da furucin da gwamnatocin da su ka gabace ta su ka yi na cewa; Yankin tuddan Gulan yaka karkashin Ira’ila ne, MDD ta bakin mai Magana da yawun babban magatakardarta cewa; Tuddan Gulan mallakin Syria ne wanda aka mamaye.

Kakakin babban magatakardar MDD, Farhan Haqq, ya ce; Tuddan gulan na kasar Syria ne da aka mamaye, yana mai kara da cewa; babu abinda ya sauya akan wannan yanayin na yankin.

Wakiliyar Amurkan a MDD Linda Thomas ta ce; gwamnatin Amurka da ta gabata ta yi furuci a 2019 cewa, yankin Gulan na Isra’ila ne, don haka yar yanzu wancan furucin yana aiki ba tare da wani sauyi ba.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump shi ne wanda ya bai wa HKI yankin na tuddan Gulan a cikin watan Maris na 2019,wanda a wancan lokacin ya fuskanci mayar da martani mai tsanani.

Tun a 1967 ne dai HKI ta mamaye tuddan Gulan, kuma duk da cewa;MDD tana daukar yankin a matsayin na Syria, sai dai har yanzu ‘yan sahayoniyar sun ki janyewa daga cikinsa.

 

©Htv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “MDD Ta Mayar Wa Da Amurka Martani Akan Yankin Tudun Golan Dake Karkashin Mamayar HKI”