February 9, 2023

MDD: Sama da mutane miliyan 8.3 na bukatar tallafin jin kai a Somalia

MDD: Sama da mutane miliyan 8.3 na bukatar tallafin jin kai a Somalia

Ofishin MDD mai lura da ayyukan jin kai ko OCHA a takaice, ya ce adadin al’ummar Somalia dake bukatar agajin jin kai ya haura mutum miliyan 8.3, a gabar da kaso mai yawa na al’ummar kasar ke fuskantar matsalar fari.
OCHA ya ce idan aka ci gaba da fuskantar karancin kudade, da rashin managarcin tsarin tallafawa, ’yan kasar da dama na iya tsunduma cikin fari, tun daga watan Afrilu zuwa Yuni, musamman a yankin kauyukan Baidoa da Burhakaba, da kuma sansanoni wadanda suka rasa matsugunan su dake Baidoa da Mogadishu.
Ofishin na OCHA ya kara da cewa, ko da ma ba a fuskanci fari ba, al’ummu da dama a Somaliya na cikin matsanancin yanayin jin kai, duba da cewa sama da ’yan kasar miliyan 6.3 na fuskantar mummunan yanayi na kamfar abinci tsakanin watannin Janairu zuwa Maris, ciki har da mutane 322,000 dake cikin mummunan yanayin karancin cimaka.
OCHA ya kuma yi kashedin cewa, adadin mace-mace da ake hasashen samu na iya kaiwa na shekarar 2011, lokacin da kusan al’ummar kasar 260,000 suka rasu, kuma a kalla rabin su kananan yara ne.
A shekarar 2022 kadai, yaran Somaliya 1,049 ne suka rasu a cibiyoyin samar da abinci mai gina jiki dake kasar, baya ga karin wasu da dama da ba su ma samu damar zuwa cibiyar ba.
OCHA ya alakanta dalilin aukuwar hakan da kamfar ruwan sama da aka samu a Somaliya damuna 4 a jere, da tsawaitar tashe-tashen hankula, da yawan mutane masu kauracewa gidajensu, da tsadar kudaden abinci, wanda ya jefa miliyoyin jama’a cikin hadari, tare da ingiza da dama cikin matsalar fari.

©(Saminu Alhassan)

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “MDD: Sama da mutane miliyan 8.3 na bukatar tallafin jin kai a Somalia”