September 21, 2021

Matsin Rayuwa: Sanusi Lamido Ya Nemi ‘Yan Najeriya Da Su Kauracewa Zagin Shuwagabanni

Daga Abubakar Sadiq Ibrahim


Tsohon sarkin kano kuma halifan darikar Tijjaniya a Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi ya kalubalanci yan Najeriya kan suka da tsinuwa da suke yawan yi ma shuwagabannin su kan matsin taltalin arziki da wahalhalun rayuwa da suke fuskanta a kasar.

Ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana da wasu mabiyan darikar daga wasu jahohi na Arewa maso yammacin kasar a yau talata, ya kuma kara masu kwarin gwiwa da yin bushara da canzawan lammura a nan gaba kadan a kasar.

Ya bayyana cewa a tashi fahimtar dole sai an fuskanci yanayi maras dadi kafin isa zuwa ga yanayin da ake fata, a bayanin nasa ya nemi al’umma da su ci gaba da hakuri kana kuma da addua sannan yayi ishara ga al’ummar da su tashi tsayin daka don gyara abubuwa ta bangaren su.

Cikin bayanin nasa halifan ya bayyana cewa wajibin mu ne mu kaurewa zagi ko tsinuwa ga shuwagabannin mu saboda manzo ya hane mu da aikata hakan. Ya kuma ce dole mu canza kawunan mu don zama jakadun kirki da yada zaman lafiya da cigaba a duk inda muka tsinci kan mu.

Kana ya nemi hadin kan al’ummar muslumin ya kuma shawarci kungiyoyin addini da su samar da makarantu da kuma cibiyoyin koyon sana’a don mabiyansu su zama masu dogaro da kai.

A karshe kuma ya karfafi al’ummar muslumi da su cigaba da gudanar da lamuran addini kamar yadda manzo ya koyar, kana kuma ya hore su da sanya kai cikin abubuwan da zasu haifar da rarraba da rashin jituwa tsakanin musulmi.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Matsin Rayuwa: Sanusi Lamido Ya Nemi ‘Yan Najeriya Da Su Kauracewa Zagin Shuwagabanni”