October 11, 2021

Matsin lamba: Masu garkuwa da mutane na neman dafaffen abinci madadin kudin fansa

Daga Fatimah Mardiyya Kawo


Matsin lamba da tsauraran matakai da ake cigaba da dauka kan masu garkuwa da mutane da sauran yan bindiga a yankunan Arewa maso yammacin Nijeriya na sanya yan bindigan hali maras dadi inda yunwa ke kara ta’azzara.

Rahotanni daga mazauna yankunan na Arewa maso yamma musamman karamar hukumar Birnin Gwari da ke jahar Kaduna ya kara tabbatar da hakan.

Rahoton ya nuna cewa an samu saukin garkuwa da mutane a yankin tun bayan matakin da gwamnatin jahar ta dauka na hana cin wasu kasuwannin mako.

Wasu mazauna kauyukan na Birnin Gwari sun shaida cewa tun wannan mataki da aka dauka yan bindigan sun rage aiyukan da suka saba yi a kauyukan Kutemashi, Kuyello da kuma kauyen Damari, kana kuma sun daina tambayar kudaden fansa bayan sun yi

garkuwa da mutum, a maimakon hakan sukan tambayi dafaffen abinci don su saki wanda suka yi garkuwa da su din.

A bangare guda kuwa matakin hana sayar da man fetur a wasu wuraren ya taimaka wurin rage zirga-zirga yan bindigan.

Mazauna yankin sun bayyana cewa akwai cigaba sosai a bangaren tsaro tun bayan wadannan matakai da aka dauka.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa da yawan lokaci yan bindigan kan saki mutum guda daga mutanen da suka yi garkuwa don ya dawo gida ya kai masu dafaffen abinci a maimakon kudin fansa, hakan yakan faru saboda babu layukan sadarwa da zasu iya tuntubar yan uwan wadanda suka yi garkuwa da su.

Sai dai kuma ya bayyana cewa a bangare guda yan kauyen na wahala sanadin hana amfani da baburan hawa na kai-da-kai.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Matsin lamba: Masu garkuwa da mutane na neman dafaffen abinci madadin kudin fansa”