November 30, 2021

Matsayin Imam Hasan (a.s) Na Ilimi

Daga Muhammad Awwal Bauchi


Tarihi bai taba ba mu labarin wani al’amari da saninsa ya rikicewa Ahlulbaiti (a.s.) ba, ko amsar wata tambaya da ta gagare su amsawa ba. Su ne suka sami daukakar mutuntaka da taimakon Allah Madaukaki, har suka isa zuwa kamalar ruhi ta yadda waninsu bai kai su ba bayan Manzo (s.a.w.a).

Duk wanda ya kalli abubuwan da muka gada daga gare su, ya kuma yi nazarin abubuwan da aka ruwaito na tunane-tunane da ra’ayoyinsu zai riski zurfin iliminsu da cikar masaniyarsu.

An taba ce wa Imam Hasan (a.s.): Mene ne gudun duniya?

Sai ya ce: “Kwadayin tsoron Allah da tsentseni (a al’amuran) duniya”.

Sai aka ce masa: Mene ne hakuri?

Sai ya ce: “Hadiye fushi da mallakan kai”.

Sai aka ce masa: Mene ne tabbata?

Sai ya ce: “Kore mummunan abu da abin kirki”.

Sai aka ce masa: Mece ce daukaka?

Sai ya ce: “Sana’anta dangi da daukar dawainiyar wasu”.

Sai aka ce masa: Mene ne zama gagara-badau?

Sai ya ce: “Kariya ga makoci da yin hakuri a inda ya kamata, da gabata a lokacin da mutane ke nokewa”.

Sai aka ce masa: Mece ce kyauta?

Sai ya ce: “Ka bayar cikin himma, ka yafe laifin (da aka yi maka)”.

Sai aka ce masa: Mene ne mutumci?

Sai ya ce: “Kiyaye addini da mutunta kai, saukin kai, akawarin alheri, sadar da hakkoki (ga masu su) nuna kauna ga mutane”.

Haka nan wani mutum ya taba tambayarsa cewa: Me ke tsakanin shiriya da bata?

Sai ya ce: “Abin da ke tsakanin ‘yan yatsu; domin abin da ka gani da idonka shi ne gaskiya. Kana iya jin barna da yawa ([1])”.

Wannan karamin misali ne na iliminsa. Mai son karin bayani na iya komawa litaffan da suka fadada.

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Matsayin Imam Hasan (a.s) Na Ilimi”