December 16, 2021

Matsalar tsaro: Kasar China zata aiko da kwararrun masu binciken laifuka zuwa Nijeriya

Rahoton kamfanin dillancin labarai


 

A sabili da matsalolin rashin tsaro da ke addabar kasar Nijeriya, kasar China ta yi wa gwamnatin tarayyar Nijeriya tayin kwararru na musamman kan binciken laifuka don ganawa da kuma yin aiki hannu-da-hannu tare da jami’an tsaron Nijeriya.

Jakadan kasar China a Nijeriya, Ciu Jiuanchun, shine ya bayyana hakan a jiya Laraba a barninin tarayya Abuja a yayin ganawarsa da ‘yan jaridu kan fashin bakin karramawar da aka yi ta kawancen kasasahen Nijeriya da China a daliban jami’ar Ahmadu Bello dake zariya a ranar 1 ga watan Oktoban da ta gabata.

Jakadan ya bayyana cewa, wannan yunkurin na kasar China na daga gudunmawarta ga Nijeriya kan tabarbarewar lamuran tsaro, a sabili da haka, ana tsammanta isowar jami’ai na musamman kuma kwararru a bangaren bincike daga China zuwa Nijeriya nan ba da jimawa ba.

Inda yace “Gwamnatin kasar China ta damu sosai da yanayin tsaro a Nijeriya, kana kuma da yan kasar China mazauna Nijeriya.

“A halin yanzu haka muna iya bakin kokarin mu don ganin ta wanne hanya zamu samu agaji daga China, a tunanina, wannan ya shafi kowanne dan Nijeriya, kuma inada imanin cewa, wannan ba lamari ne kan Yan Nijeriya da gwamnatin Nijeriya kadai ba, akwai bukatar agajin kasa-da-kasa.

“A bisa wannan dalilin, gwamnatin China ta yanke cewa zata aiko kwararrun masana daga bangaren binciken laifuka zuwa Nijeriya.

“Zasu zo Nijeriya su mu’amalantu da al’umma, gwamnati kan yadda zasu yi aiki tare don shawo kan kalubalen da ke fuskanto Nijeriya.

“Shugaban jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Kabiru Bala ya yi godiya ga gwamnatin kasar China kan agajin ta ga Nijeriya a kokarin dakile matsalolin tsaro na kasar.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Matsalar tsaro: Kasar China zata aiko da kwararrun masu binciken laifuka zuwa Nijeriya”