September 11, 2021

Matsalar Tsaro: An Hana Sayar Da Gidaje Ba Bisa Lamunin Hukuma Ba A Kano

Daga Muhammad Bakir Muhammad

 

Gwamnarin jihar Kano fitar da dokar cewa dole a bi dokoki da kuma samun yardar wakilan hukuma (hakimai ko wakilan su) kafin sayar da gida ko bada haya a duk fadin jahar.

A ranar juma’a ne sakataren yada labarai na maga takardan gwamnatin jaha, Musa Tanko Muhammad ya bayyana cewa wannan matakin na daga kokarin gwamnatin jaha na tsare lafiyar al’ummar jahar da kuma dukiyoyin su.

Ya bayyana kuma cewa kiyaye wannan doka wajibi ne saboda taimakawa jami’an tsaro a kokarin su na dakile matsalolin tsaro da aiyukan yan bindiga da bata gari a fadin kasar nan.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Kano ta dau wannan matakin ne don bai wa gwamnatin tarayya gudunmawa a kokarin da take na kawo karshen rashin zaman lafiya a wasu sassan kasar, inda yace bata garin zasu iya neman guraren fakewa a jahohin ketare wanda kuma Kano na daya daga ciki.

Ya bayyana cewa gwamnati ta bada umarnin cewa babu wani gida da za’a sayar ko bada haya ga wani ko wasu mutane ba tare da lamanin hakimai ko wakilan su ba.

Daga karshe kuma yayi kira da babban murya ga dilllalan filaye da gidaje kan su bi dokokin da aka shimfida musu inda kuma kin hakan ka iya jan hukunci mai muni.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Matsalar Tsaro: An Hana Sayar Da Gidaje Ba Bisa Lamunin Hukuma Ba A Kano”