September 27, 2021

Matsalar Tsaro A Najeriya: Hukumar “Navy” Ta Zargi Sojojin Chadi

Daga Isah Musa Muhammad


Hukumar sojan ruwa na kasar Najeriya ta zargi sojojin Chadi da sayar da makamai ba bisa ka’Ida ba.

Wakiliyar shugaban hukumar “Navy”, Commodore Jemila Abubakar ce ta bayyana hakan a yayin da ta wakilci shugaban hukumar; Awwal Gambo, a wani taro da kamitin majalisar wakilai ta shirya kan lamarin tsaro.

A yayin da take bayani kan yawaitar kanana da manyan makamai, ta bayyana bayyana cewa tallafin makamai da manyan kasashen duniya ke bayarwa makobta na haifar da manyan matsaloli kan harkokin tsaro na kasar.

Commodore Jemila ta bayyana cewa tana daya daga wadanda suka kasance gaba yayin yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram, saboda haka tana da masaniyar cewa yawancin kasashen ketaren Najeriya basu da ma’ajiyar makamai.

A bangare guda kuwa manyan kasashen duniya ke basu tallafin makamai da sunan suna taimakon su alhali anan Nageriya hakan na sake lalata harkokin tsaro.

Wasu lokutan zaka iske tsaka–tsaki daga sojojin Chadi ya mallaki bindigogi 20 zuwa 30 wadanda ke boye karkashin katifar sa, a saboda haka idan ya shiga halin rashin kudi sai ya fara sayar da su akan kudade dalan Amurka $30, $20 da sauran su, kana kuma ta tabbatar da cewa tana fadin hakan ne bisa yakini da hujja.

Ta nemi a zanta da gamayyar kasashen Afirka ta yamma (ECOWAS)da sauran kasashen duniya kan su samar da mafita ga lamarin, imma gina masu wurin adana makamai ko kuma a dena turamasu tallafin makamai.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Matsalar Tsaro A Najeriya: Hukumar “Navy” Ta Zargi Sojojin Chadi”