April 20, 2023

Matashin Da Ya Je Masallacin Kudus A Kafa Daga Faransa

 

Masallacin Kudus shi ne na uku wajen falala a addinin Musulunci. Wani matashi da ya taka a kafa daga kasar Faransa ya isa Masallacin bayan wata 10.

Neil Dauxois dan shekara 26 ya yi tafiyar kilomita 3,900 inda ya ratsa ta kasashe 10 kafin ya isa Masallacin Kudus, inda ya samu gagarumar tarba daga Falasɗinawa.

Masallacin Kudus shi ne na uku wajen falala a addinin Musulunci, kuma an kwadaitar da ziyartarsa.

Isarsa Birnin Kudus ke da wuya, al’ummar Musulmai Falasdinawa suka yi ta maraba da shi suna gayyatar sa zuwa gidajensu, inda suka shirya masa liyafa.

Ya ce, “Da farko mahaifiyata ta damu, amma bayan da ta ga hotunana a kafofin sada zumunta, sai ta bayyana alfaharinta da ni.”

Kasashen da ya wuce bayan ya fara tafiyar daga Faransa sun hada da Italy, Slovenia, Croatia, Bosnia-Herzegovina, Montenegro, Albania, Greece, Türkiye, Cyprus da Jordan kafin ya isa birnin Kusus.

“Falasinawa da yawa sun yi ta gayyata ta zuwa gidajen; Na yi mamakin hakan, kuma na yi farin ciki sosai,” in ji shi, bayan isarsa Birnin Kudus.

Neil wanda dan asalin kasar Aljeriya ne, ya ce, burinsa na gaba shi ne karasawa zuwa kasar Saudiyya a cikin wata biyu domin yin aikin Hajji.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Matashin Da Ya Je Masallacin Kudus A Kafa Daga Faransa”