MATAMBAYI BA YA BATA

Tare da Baban Hadiza
Shekaran jiya ina nazarin wani littafi mai suna: Hudubobin Juma’a da idodi biyu, daya daga cikin litattafan da aka tattare hudubobin maulana Shek Muhammad Nasir Muhammad limamin masallacin waje a cikin birnin Kano, wanda gwamnatin malam Ibrahim shekarau ta dauki nauyin buga shi.
Littafin yana dauke da hudubobi guda sittin da daya da mabambantan maudu’ai na tarbiyya da wa’azozi, kamar:
1 – Tasirin Zunubai da laifuka.
2 – Duban Allah a dukkanin lamura.
3 – Siffofin Musulmi.
4 – Tsoron Allah.
5 – Tsakanin hankali da nassi.
Da sauransu.
Ganin yadda aka kayata littafin, sai tunanina ya kawo cewa: Ai shugaban halitta annabi Muhammad (s.a.w) ya shekara goma a Madina, kuma shi ma yana yin huduba duk juma’a fiye da mako dari biyar, sai shaukin karanta hudubobin nasa ya kama ni, na fara yin cigiya a tsakanin ‘yan uwa almajirai ko Allah zai sa in dace da samun su, Allah ya datar da mu.
Allah ya sanya mu a cikin ceton annabinsa Muhammad (s.a.w)