MATAKI NA HUDU AMFANI DA DAMA

Sirrin Samun Nasara
Kowannenmu ya san cewa kowane abu a cikin wannan rayuwar mai karewa ne, rana tana karewa da zuwan dare, karfi yana karewa ya zama rauni, kuruciya tana komawa tsufa, mutum yana komawa kasa, dukkan wani abu da yake a wannan rayuwar yana komawa zuwa kishiyarsa.
Hakika damar da mutum yake samu ba ta dauwama, idan kuma ta kubuce masa ba ta komowa gare shi har abada. Kamar yau din da muke ciki sai ta kare ta koma jiya, gobe kuma sabuwar rana ce, kamar yadda ya zo a ruwaya a littafin Manla yahdurul fakih, j4: 297 cewa:
(ما من يوم يأتي على ابن آدم إلا قال له ذلك اليوم: يا ابن آدم أنا يوم جديد وأنا عليك شهيد، فقل فيّ خيرا واعمل فيّ خيرا اشهد لك به يوم القيامة فإنك لن تراني بعد هذا أبدا).
Babu wata rana da za ta zo wa mutum face sai ta ce da shi: Ya kai mutum, ni ce sabuwar rana, kuma zan yi maka sheda, ka fadi alheri a cikina, kuma ka aikata alheri a cikina, zan shede ka da wannan a ranar Alkiyama, domin ba za ka sake ganina ba bayan wannan.
A nan za mu fahimci muhimmancin samun dama da kuma yin amfani da ita. Mai hikima shi ne yake amfani da damarmaki yake amfani da su a wajen aikata alheri, wanda kuwa ya gafala daga amfani da ita, ko ya kasance ya same ta ba tare da ya yi amfani da ita yadda ya dace ba, to babu abin da zai girba sai karin asarori da bakkan ciki.
Wani mai hikima yana cewa: Dama kamar girgijen damuna ce wanda yake dauke da ruwa, yana da kyawun gani, sai dai yana saurin gushewa, wanda yake son amfana da ruwansa sai ya yi kokarin tanadin kayan taren ruwa, idan ya sauka zai zama ya tari ruwan saman mai yawa.
Amma wanda yake bukatar ruwa kuma yana kallon hadari a samansa yana wucewa ba tare da ya tanadi abin tara ba, to yana bata lokacinsa ne domin zai yi asarar abubuwa biyu: Lokacinsa da kuna ruwan gaba daya.
To haka dama take yin tafiyar girgije, tana da saurin gushewa ba ta komowa, duk wanda yake bukatarta to sai ya yi mata shirin ribatarta, idan ba haka ba kana kallonta za ta zo ta wuce ba tare da ka ribaci komai a cikinta ba.
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Duk wanda aka bude masa kofar alheri to ya ribace shi, domin bai san lokacin da za a kulle masa kofar ba.
Haka nan ya zo a cikin littafin: Wasa’il: j1: 114. Manzon Allah (s.a.w) yana yi wa Abuzar wasiyya cewa: Ya kai Abazar, ka ribaci abubuwa biya kafin zuwan abubuwa biyar:
– Kuruciyarka kafin zuwan tsufanka.
– Lafiyarka kafin zuwan rashin lafiyarka.
– Wadatarka kafin zuwan talaucinka.
– Damarka kafin kubucewarta.
– Rayuwarka kafin mutuwarka.
Wannan ruwayar tana karfafa mana muhimmancin ribatar damarmaki da suke zowa mana a rayuwa, wato: Kuruciya da lafiya da wadata da lokaci da kuma rayuwa.
DAMA TA KURUCIYA
1 – Kuruciya dama ce, tana ma daga cikin mafiya muhimmancin damarmaki a rayuwar mutum da ya kamata ya ribace ta domin ya kai ga gaci, ta yadda zai samu kamala da yalwa da ci gaban rayuwarsa, bayan haka kuma zai koma gangara ne zuwa ga yin rauni.
Tsoho ba zai taba dawowa saurayi ba, duk da yake kadan ne suka fahimci muhimmancin wannan dama da kuruciya, mafiya yawa sai bayan sun rasa ta suke yin nadamar more rayuwa da suka yi tare da takaitawarsu, wannan yana iya zama shi ne mafi munin kuskuren da mutum yake yi game da wannan dama ta kuruciya na rashin amfana da ita.
A ranar alkiyama za a yi wa rayuwa hisabi na musamman, kuruciya ma a yi mata hisabi na musamman. Wadanda suka yi asarar samartakarsu ba sa fahimtar zurfin laifin da zuka aikata wa kawukansu sai bayan an kada musu karaurawar tsufa! Ga shi kuma kuruciyar ta tafi babu dawowa!!
©✍ Mujtaba Shu’aibu Adamu