Mata sun yi zanga-zanga a Abuja kan sakamakon zaɓe tare da yin barazanar tafiya tsirara

Wasu fusatattun mata, a karkashin kungiyar ‘Angry Nigerian Women’ a yau Talata sun mamaye babban titin da ke kan hanyar zuwa babban dakin taro na kasa da kasa, wurin da ake tattara wa da sanar da sakamakon zaben shugaban kasa, bisa zargin tafka magudi.
Jaridar Punch ta rawaito cewa matan sun kuma yi barazanar za su tafi tsirara idan har hukumar zabe mai zaman kanta ta ki amincewa da bukatarsu kan dalilin da ya sa ba a aika sakamakon zaben shugaban kasa ta hanyar yanar gizo zuwa babban dakin tattara sakamakon zaɓe na INEC yadda kowa zai gani.
Matan da ke rera wakoki irin su ‘ba mu yarda ba’, ‘Mahmood ya nuna mana sakamako’, ‘asali sakamakon da muke so’ suma suna dauke da alluna dauke da rubuce-rubuce daban-daban da suka hada da, ‘INEC ki dena magudi’, ‘makomar ‘ya’yan mu muke ji, ‘Mahmood ka bamu sakamakonmu’, ‘mun gaji da zalunci’