October 29, 2022

Mata kenan Tana kwance akan shimfiɗar ajali ta ce, Habibina in na mutu zuwa yaushe zaka sake wani auren?

Mata Kenan….

Tana kwance akan shimfiɗar ajali ta ce, Habibina in na mutu zuwa yaushe zaka sake wani auren?

Yana kuka ya ce, zuwa lokacin da ƙasar kabarinki zata bushe. Ta yi murmushi ta ce, ka yi alƙawari? Ya ce, ƙwarai ma kuwa.

Bayan ta rasu sai da ya shafe fiye da shekaru 5 ya na zuwa maƙabarta amma abin mamaki kabarin bai bushe ba.

Allahu Akbar, ya yi mamaki sosai kuma ya ƙudurce a ransa matarsa Waliyyiya ce.

Wata rana ya yi sammako don ziyarar kabarinta, sai ya ci karo da ɗan uwanta, suka gaisa. Ya ce kazo ziyarar ƴar uwarka ke nan?

Sai ya ce na dai zo don cika wasiyyar da ta mutu ta bar mini. Ta yi mini wasiyyar kullum da sassafe nazo na jiƙa ƙasar kabarinta, hakan zai sanya ta kwanta cikin nutsuwa, shekara da shekaru kenan ina wannan aikin.

Wani aikin sai mata…

SHARE:
Tattaunawa 0 Replies to “Mata kenan Tana kwance akan shimfiɗar ajali ta ce, Habibina in na mutu zuwa yaushe zaka sake wani auren?”