Masu zanga-zanga sun yi Qunuti da sallah Ofishin INEC na Potiskum

Biyo bayan zaben da ya gudana a shiyar Yobe ta kudu a ranar Asabar, har yanzu hukumar INEC bata sanar da wanda ya lashe zaben dan majalisar dokoki na yankin ba duk da alkaluma sun nuna inda sakamakon ya dosa tun da farko.
Biyo bayan shirun da aka ji, magoya bayan dan takarar dan majalisar dokoki a jami’iyar PDP wato Halilu Mazagane sun yi cincirindo a ofishin INEC da ke garin Potiskum ta jihar Yobe.
Tun farkon zanga-zangar, an jibge jami’an soja da na yan sanda don kwantar da tarzoma sai dai kuma jama’an sun ki watsewa sun kuma nemi da INEC ta sanar da wanda yayi nasara ba tare da murdiya ba.
Da maraicen nan ne aka gano masu zanga-zangar na gudanar da sallah da kuma Al-kunuti a bakin ofishin na INEC Potiskum..