October 10, 2023

MAS’ALOLON FIƘIHUN SHI’A IMAMIYYA.

Sheikh Amjad Mukhtar

Kokonto A Cikin Sallah,
Kokonto a cikin sallah ya kasu kashi biyu:
– Na farko kokonton dake ɓata sallah baya yiwuwa a gyara.
– Na biyu kokonton da ake iya gyara shi.

Kokonton Dake Ɓata Baya Yiwuwa A Gyara Sune Kamar Haka:
1 – Shakku a cikin adadin raka’oin sallar asuba (Ai yana shakka, shin a raka’a ta farko nake kota biyu, to sallar ta ɓaci indai a sallar asubah ne baya yiwuwa a gyara ta, saidai ya sake wata).
2 – Shakku a cikin adadin raka’oin sallar magriba. (Ai shakka yake, shin a raka’a ta farko nake, kota biyu kota uku, sallar ta ɓaci indai a sallar Magriba ne, saidai a sake wata).
3 – Shakku a cikin raka’oi biyun farko na sallah mai raka’a hudu. (Ai shakka yake, shin a raka’a ta farko nake kota biyu, a sallah mai raka’a huɗu, to sallar ta ɓaci saidai a sake wata).
• Duka wadannan shakku suna ɓata sallah baya yiwuwa a gyara su.

Kokonton Da Ake Iya Gyara Su Kuma Sallah Ta Inganta Sune Kamar Haka.
1 – Kokwanto tsakanin raka’a ta biyu da ta uku, bayan zikirin sujjadar ƙarshe, a wannan lokacin zai gina akan cewa a raka’a ta uku yake, sannan ya zo da ta hudu, ya cika Sallar sa, sannan ya zo da raka’a daya ta ihtiyadi a tsaye. A bisa ihtiyadi wujubi (na wajibi).

2 – Kokonto tsakanin raka’a ta uku data huɗu, ako wane mahalli yake a cikin sallar, zai gina ne akan cewa ta hudu yake, sannan yayi raka’oin ihtiyadi biyu a zaune ko raka’a ɗaya a tsaye.

3- Kokwanto tsakanin raka’a biyu da hudu, bayan zikirin sujjadar karshe. Zai gina ne akan cewa yana raka’a ta hudu ne, sai ya cika Sallar sa, ya yi sallama sannan ya yi ihtiyadi da raka’o’i biyu a tsaye (wato ya tashi yayi raka’atul ihitiyaɗi raka’a biyu a tsaye).

4- Shakku tsakanin raka’a biyu da uku da hudu, bayan zikirin sujjadar
Ƙarshe, zai cika Sallar sa sannan ya yi ihtiyadi da raka’o’i biyu a tsaye sannan ya kuma yi guda biyu a zaune.

5- Shakku tsakanin raka’a hudu da biyar bayan zikirin sujjadar ƙarshe, zai gina ne akan yana raka’a ta hudu ne, sannan ya yi sujjadar rabkanuwa. ya cika Sallar sa.

6- Shakku tsakanin raka’a hudu da biyar a halin tsayuwa. Anan zai rusa tsayiwar (ma’ana zai zauna) hukuncin sa, hukuncin mai shakku tsakanin uku da hudu ne, sai ya cika Sallar sa ya yi ihtiyadi da raka’o’i biyu, a zaune.

7- Shakku tsakanin raka’a uku da biyar, a yayin tsayuwa, a sannan zai rusa tsayuwar (ya zauna) hukuncin sa hukuncin kokwanto tsakanin biyu da hudu ne, sai ya cika Sallar sa ya yi ihtiyadi da raka’a biyu, a tsaye.

8 – Shakku tsakanin raka’a uku da huɗu da biyar a yayin tsayuwa, mutum zai rusa tsayuwar (ya zauna) hukuncin sa hukuncin mai kokonto tsakanin raka’a biyu da uku da huɗu ne, zai gina akan raka’a ta huɗu yake, sai ya cika sallar sa, kuma yazo da raka’oi biyu a a tsaye na ihitiyaɗi, kana yayi raka’oi biyu a zaune.

9 – Shakka tsakanin raka’a biyar da shida a yayin tsayuwa, zai rusa tsayuwar ya zauna, hukuncin sa hukuncin mai shakka ne tsakanin raka’a huɗu da biyar, sai ya cika sallar sa yayi sujjadar rafkanwa.

A Rubutu Na Gaba Zamu Kawo Yadda Ake Sallar Ihitiyaɗi Da Sujjadar Rafkanwa Insha Allah.

SHARE:
Makala 0 Replies to “MAS’ALOLON FIƘIHUN SHI’A IMAMIYYA.”