September 19, 2021

Mas’alolin Fiqihu

Daga mimbarin:

Hujjatul Islam wal muslumin, Sheikh Muhammad Nur Dass (H)


Tambaya:
Salam. Don Allah malam ina hukuncin sallah bisa kafet (darduma) a masallacin Sunnah, da kuma sallar Magriba da Isha’i tare da su alhali rana bata fadi ba bisa hakika?

AMSA:
Salam, yin sujjada a bisa shimfida, misali darduma a masallacin ‘yan Sunnah domin takiyya da kuma hadin kai (wahda) bai da matsala, halas ne yin haka, kana irin wannan ibada da kayi ta inganta.

Salam, bin su sallah yana daga cikin mustahabbi mai karfi, cewa da kayi bin su sallah alhali lallai rana ba ta fadi ba, wato ina hukuncin yin sallah kafin shigar lokacin ta, to idan kana da yakini (wato tabbacin) cewa lokaci bai yi ba, amma sai ka bi su, to a wannan yanayi zaka sake sallah, sai dai idan shakku ne gare ka (dangane da shigar lokacin) amma bai kai ga yakini ba, to sallarka ta inganta.Tambaya:
Assalam Alakum ya Sheikh, yaya matsayin wanda aka haifa kafin a yi aure a musulunci? kuma yaya sunan sa a musulunci? Kana ya halasta ya ci gado? Ka huta lafiya.

AMSA:
Salam, ‘Dan da aka haifa ba tare da aure ba ta hanyar fasikanci ne da yin taurin kai wa shari’a, to ya zama ‘Dan haram, amma idan bisa shubuha (kuskure) ne misali jahilci ne ya kai su ga haka ko bisa rabkannuwa, to wannan bai zama ‘Dan haram ba.
A halin zina ana kiran wannan ‘Da da suna ‘Dan zina, amma a halin shubuha (kuskure) ana kiran irin wannan ‘Da da suna ‘Dan shubuha.
‘Dan zina ba ya gado, amma ‘Dan shubuha yana gado.

SHARE:
Mas'alolin Fiqihu 0 Replies to “Mas’alolin Fiqihu”