Ahlul Baiti

Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)

October 8, 2021

Mas’alolin Fiqihu

Daga mimbarin Hujjatul Islam wal muslumin 

Sheikh Muhammad Nur Dass (H)


Tambaya
Salam, Malam dan Allah ina son a yi min bayani a kan dalilin hada sallar Zuhur da Asr, da kuma Magrib da Isha.
Bissalam, ka huta lafiya.

AMSA:
Salam, hada Azahar da La’asar, kana da Isha’i yin haka a mazhabar Imamiyya abu ne wanda ijtihadi ya zo da shi, sannan saukakawa ne ga mukallafi, amma ba wajibi ba ne.
Ga duk wanda ya so ya yi riko da wannan rangwame da shari’a ta yi, to yana da dukkan damar yin haka. Zai kuma samu a kur’ani, misali ayoyi da ke ambaton lokutan sallah uku:
“A’kimis salati li-dulukish-shamsi ilaa gasakil-laili wa ‘kur’anal fairi…”


 

Tambaya:
Salam malam ni makiyayi ne, muna kiwon kajin gidan gona ni da wani abokina dan Sunnah, sai ya ba da shawarar mu hada da kiwon kifi amma tarwad’a, duk da na yi masa bayanin matsayin tarwad’a a wajenmu, sai ya ce min ya ji, amma su ai suna ci, sai nace masa ai hatta su din ma bai halasta su ci ba. Sai ya ce, to sai mu kai Kudu jihohin da ba na musulmi ba, tambaya ta anan ita ce, Malam, shin hakan ya halasta? Na gode, a huta lafiya.

 

Amsa:
Salam, Hukuncin sayar da kifi wanda ba shi da kaushin baya irin tarwad’a yana daidai da hukuncin sa, wato babu halasci matukar za ka sayar ne domin a ci, amma idan za ka sayar wa kamfanin yin sabulu ne da wata manufa ta daban, wato domin a sarrafa a yi sabulai da shi, to wannan halas ne.


 

Tambaya:
Salam, Malam mene ne hukuncin tsintuwa? Domin na taba tsintar kudin da suka kai naira dubu 150,000 a kan hanyata ta zuwa gida kuma lokacin ba kowa a wurin, na d’an tsaya don ko wani zai zo yace na shi ne amma ba wanda ya zo, a gefe guda kuma dama ina da tsananin bukatar kudin, Malam kawai sai na ci gaba da hidimata da su, kuma sai daga baya aka ce sai na biya, Tun da ni dai yanzu ba ni da su, kuma malam wa zan bawa tun da ni dai har yanzu ban san mai kudin ba.

Allah ya saka da alheri, ya kara lafiya.

Amsa:
Salam, idan abinda ka tsinta yakai dirhami daya (wato gram na azurfa biyu da digo shida, 2.6) ko fiye da haka to wajibi ne a sanar harna tsayin shekara guda matukar ba ka debe tsammanin samun mai shi ba, idan kuwa ka debe tsammanin samunsa, to ya halasta ka mallake kudin, da niyyar cewa duk lokacin da aka samu mai shi, za ka mayar masa.
Kana zaka iya yin sadaka da shi sai ka wakilci mai shi wajen bayarwa ga fakirai. Kamar yadda kana iya ci gaba da rike masa shi a wurinka, a matsayin amana.

SHARE:
Mas'alolin Fiqihu One Reply to “Mas’alolin Fiqihu”
Ahlul Baiti
Ahlul Baiti

COMMENTS

One comment on “Mas’alolin Fiqihu

    Author’s gravatar

    Assalam malam barka da yini,ya ayyukha da fatan kuna cikin lfy. Malam tambayata anan itace shin Yaya ake cire kumusu daga cikin kudin da aka juya su day kasuwansu har tsawon shekara guda kuma kudin sunkai darajar dubu uku a sanda aka fara sana’ar Amma yanzu sunkai dubu dari biyar da shashida

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *