Ahlul Baiti

Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)

September 21, 2021

Mas’alolin Fiqhu

Daga mimbarin Hujjatul Islam wal muslumin: Sheikh Muhammad Nur Dass (H)


Tambaya:Salam ya maulana, Malam nine muka daura auren tamattu’i da wata baiwar Allah, amma lokacin da za mu daura auren sai tace ta walkilta ni don in wakilce ta wajen bayarwa (ijabi), sannan kuma ni in karba wa kaina (Qabuli), kuma hakan aka yi, shin malam yaya auren namu yake?

 

AMSA:
Salam, A mazhabar Ahlulbaiti (wato Imamiyyah), wannan aure naku ya inganta domin tana da zabi ko ita ta bayar, ko miji ko wakilin miji ya karba, ko kuma ta walkilta miji ko waninsa wajen bayarwa, kana kafa shaida a daurin aure ba wajibi bane a Imamiyyah, sabanin sakin aure shi kam wajibi ne a kafa shaidu biyu adilai, idan babu su, to saki bai inganta ba.Tambaya
Salam, 1. Yaushe ake yi wa yaro kaciya (shayi) ranar suna (7) ko kuma za a iya jinkirtawa har ya girma?
2. Shin ya halatta a yi wa mata kaciya kamar yadda wadan su al’umma suke yi wa jariran su mata?

 

AMSA:
Salam,
1. Kaciya wa yaro tun daga ran akwai (7) zaka iya yi amma kada a bari ya yi watanni, kuskure ne jinkirta kaciya.
2. Kaciya wa mata ba wajibi ba be, sai dai babu haramci dangane da haka idan ba zai cutar ba.Tambaya:

Salam, Malam mene be hukuncin shan rubutu da daura laya a musulunci? Shin dagaske ne aikata daya daga cikin wadannan yana fitar da mutum daga musulunci?

 

AMSA:
Salam, Shan rubutu ba laifi ba ne, waraka ne ga mutane ta fuskoki na jiki da ruhi. Haka ma daura laya ba laifi ba ne ballantana ma ya zama shirka, misalin dukkanin su shine wanda zai sha magani domin neman waraka to ka ga ai kuskure ne don na sha fanadol a ce na bar musulunci.

SHARE:
Mas'alolin Fiqihu One Reply to “Mas’alolin Fiqhu”
Ahlul Baiti
Ahlul Baiti

COMMENTS

One comment on “Mas’alolin Fiqhu

    Author’s gravatar

    Muna taya muaaastur Rasulul aazam foundation RAAF, murnar bude wannan jarida online ta Ahlulbait.

    Muna addu’ar Allah ya kara daukaka RAAF da malamansu baki daya akan wannan kokari da sukeyi na karantarwar Aimmatu Ahlulbait (as)
    Allah ya saka da alkhairi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *