September 25, 2021

Mas’alolin Fiqhu

Daga mimbarin Hujjatul Islam wal muslumin

Sheikh Muhammad Nur Dass (H)


Tambaya:
Salam malam mutum ne ya samu raka’ar karshe tare da liman sai aka sallame, bayan su liman sun kammala sallarsu to shi ya zai yi wajen karatun raka’arsa ta karshen, a bayyane zai yi ko a boye?

AMSA:
Salam, idan ka samu raka’a ta karshe, to bayan sallamewar liman sai ka kawo raka’a daya ka yi karatu a bayyane (idan Subahi ne ko Magriba ko Isha’i) sai ka zauna ka yi tashahhud (tahiya), bayan haka sai ka sallame idan sallar asubahi ne.
Idan kuwa magrib ce ko Isha, to da ka yi wannan tashahhud sai ka tashi ka ciko raka’a daya (idan magrib ce, amma idan Isha ne raka’a biyu zaka ciko, dukkanin su a boye za ka yi karatu) sannan sai ka zauna ka yi tashahhud (tahiya) kana ka sallame.


Tambaya:
Salam, Malam mace ce ke zaune da mijin ta sai ta samu damar zuwa karin karatu a jami’a tare da izinin mijin ta, amma sai iyayenta suka ce ba su yarda ba, ita kuwa sai ta cigaba da karatunta, to yaya hukuncin hakan?

AMSA:
Salam, a wannan yanayi tun da ke matar aure ce to fitar da za ki rika yi daga gidan miji kina bukatar izinin mijinki ne, don haka ba ki aikata Haram ba a cigaba da karatun da Kika yi da amincewar mai gidanki, sai dai yana da kyau ke da shi ku ci gaba da dad’ad’a magana wa iyayenki domin su ma su fahimce ku.


Tambaya:
Salam, meye hukuncin auren mutu’a da Kirista? Kuma wacce addu’a zan yi don in yi kudi?

AMSA:
Salam, halas ne yin auren mutu’a da Ahlulkitabi, misali Kirista, sai dai mashahurin fatawa shi ne ba za a yi auren da’imi da su ba. Yin auren dindindin da su haramun ne.
Dangane da addu’ar neman kudi kuwa, yana da kyau ka yawaita yin zikirin “ya Razzaku” musamman bayan Ida da sallolin farillah.


Tambaya:
Assalam, Malam mene ne hukuncin wanda yake tare da yarinya ya nemi izinin iyayenta, Sun ki ba shi izinin tsayawa da ita, kuma saurayin da budurwar suna haduwa a wani wuri na sirri, Malam rabuwa ya kamata su yi ko yaya?

AMSA:
Salam, lallai a irin wannan yanayi idan har babu hanya ta shigar da dattijai cikin lamarin, domin su sasanta tsakaninku da waliyan yarinya, to sai ku hakura da juna, domin gudun afkawa cikin haram.

SHARE:
Mas'alolin Fiqihu 0 Replies to “Mas’alolin Fiqhu”