September 18, 2021

Mas’alolin Fikihu

Daga mimbarin Hujjatul Islam wal muslumin: SHEIKH MUHAMMAD NUR DASS (H)


Tambaya: Salam, Malam tambaya ce nake da ita guda hudu:
1. Shin da gaske ne Salatul Fatihi daga Imam Ali
(as) aka samo ta?

2. Ya halasta dan Shi’a ya yi koyi da Tijjanawa wurin zikirin wazifa?

3. Shin akwai adadi a shi’ance ga mabiyinta gurin yin istigfari ko hailala da salatin Annabi (SAWA)?

4. Ya hukuncin wanda ya yi alwala bayan ruwan sama ya jika shi? Duk da cewa ya yi iyaka kokarin sa wajen goge inda ya kamata ya yi shafa?
Bissalam!


AMSA: Salam
1. Jingina shi kocakaf ga Imam Ali da sigar da take a wajen yan uwa yan darika har yanzu bai bayyana ba. amma babu matsala ga irin wannan salati mai girmama Annabin tsira (SAWA).

 

2. Kasantuwar halartar su ga tarukan mu haka ma halartar mu ga tarukan su hanyoyi ne da ke kawo hadin kai da karfafa yan uwantaka, to muna kira ga fadada zaurukan dua’u khumail ko tawassul da sauran su domain su halarta kamar yadda a wannan babi ganinmu jefi-jefi a wannan halkoki na zikiri babu matsala.

 

3. Istigfari ko hailala da salatin Annabi (SAWA) idan ka iyakance su da adadi babu laifi, misali kace kafa 70 ko kace cikin carbi da makamancin haka, kana rashin iyakancewa shima ya halasta.

 

4. A irin wannan yanayi bayan ka goge kan ka toh matukar ruwan da ya jika kan ka bazai yi naso zuwa hannun ka ba, toh Alwala ta inganta, haka hukuncin yake dangane da kafar ka, amma idan rkuwa zai yi naso daga kan ka zuwa hannun ka ko daga kafar ka zuwa hannun ka, to zaka sake Alwala.

SHARE:
Mas'alolin Fiqihu 0 Replies to “Mas’alolin Fikihu”