October 2, 2021

Mas’alolin Fikihu

Daga mimbarin  Hujjatul Islam wal muslumin: Sheikh  Muhammad  Nur Dass  (H)


Tambaya:

Salam, malam ina son karin bayani dangane da biyan bashin sallah, kuma ana iya biyan bashin kowacce sallah a kowanne lokaci? Na gode.

 

Amsa:

Salam, haka ne ana iya biyan bashin sallah a kowane lokaci, wato ramuwar sallah ana iya yi kodayaushe. Misali sallar asubahi idan ta zama ta ramuwa, to za’a iya rama ta da dare ko da rana ba matsala, haka ma sallar azahar ko la’asar in sun zama ramuwa to ana iya rama su ko da cikin dare ne.

Kana za ka iya rama su kwana dai-daya, misali, ka fara da sallar asubahi sai azahar da la’asar sannan Magriba da isha’i (kwana daya kenan), kamar yadda zaka iya jera asuba guda biyar (na kwana biyar) sai ka jera azahar da la’asar guda biyar biyar, sannan sai Magriba da isha’i na kwana biyar.


 

Tambaya:

Salam, malam mene ne bambancin jinin haila da na istihala da na haihuwa?

 

Amsa:

Salam, Akwai bambanci a tsakanin su ta fuskoki kamar haka:

1. Jinin haila da na haihuwa suna hana ibada misali sallah ko azumi ko shafan rubutun Al-kura’ani amma jinin istihala bai hanawa.

2. Mafi karancin haila shine kwana uku, mafi yawan sa kuma kwana goma. Istihala kuwa yana wuce kwana goma.

3. Jinin haihuwa ba ya zuwa sai a lokacin haihuwa wato kafin haihuwa da kadan, har kuma bayan haihuwa amma jinin haila da istihala ana iya samun su a lokuta daban-daban na rayuwar mata. Karin bayani sai mu koma litattafan fikihu.


Tambaya:

Salam, malam ni manomin rani ne, kuma abubuwan abubuwan da nake nomawa ance ba a yi musu zalla, kamar su albasa, da karas, da shinkafa da kankana. To malam mene ne hukuncin da ya hau kaina?

Amsa:

Salam, ababen da ka ambata misali, albasa da karas da kankana da makamantan su na daga kayan lambs, to wadannan babu zakka a kan su, amma akwai wajabcin fitar da Khumusin ribar su a karshen shekara. Dangane da shinkafa kuwa to mustahabbi ne ka ba da zakkarta. Kana idan shekara ta zagayo, na is cinye ba, ya wajaba ka fitar da Khumusin abinda ya saura.

 

SHARE:
Mas'alolin Fiqihu 0 Replies to “Mas’alolin Fikihu”